Dole ne farashin man Matatar Fatakwal yayi sauki akan na Dangote—Dillalan Fetur

0
17

Dillalan fetur sun gindayawa NNPCL sharadi kafin siyan fetur daga matatar Fatakwal, dake jihar Rivers, yayin da dillalan suka ce dole ne farashin man Matatar Fatakwal yayi sauki akan farashin da matatar fetur ta Dangote, ke siyar da nata man.

A ranar Laraba ne kamfanin mai na NNPCL, yace farashin litar mai da yake siyarwa zai cigaba da kasancewa akan naira 1,045, duk da cewa har yanzu matatar ta Fatakwal bata sanar da farashin da zata siyar da kowacce litar fetur din da take tacewa ba.

:::Majalisar wakilai ta tabbatar da Olufemi Oluyede a matsayin babban hafsan sojin kasa

Rahotanni sun bayyana cewa kawo yanzu matatar Fatakwal bata fara siyarwa da yan kasuwa mai ba sai dai kamfanin NNPCL, kawai take siyarwa

Mai magana da yawun kamfanin Olufemi Soneye, yace har yanzu suna yin nazarin farashin da zasu sakawa man da suke fitarwa.

Zuwa ranar larabar data gabata, dillalan mai sun shigo da lita miliyan 105.67, na fetur cikin Nigeria, a kwanaki 5, kacal, wanda dillalan man suka ce basu da wani zabi daya wuce siyo man daga ketare saboda NNPCL yana siyar da man a farashin naira 1,045.

Yan kasuwar man sun ce farashin da NNPCL, ke amfani da shi yayi musu tsada, a yayi da Dangote ke siyar da nasa man akan naira 970, kan kowacce lita guda.

Sakataren kungiyar dillalan mai asu zaman kansu IPMAN, yace akwai bukatar NNPC, ya sake yin nazari akan farashin da yake siyarwa da yan kasuwa mai saboda yayi tsada, wanda da hakan ne yasa suke kafa hujjar cewa dole ayi wani kwakkwaran gyara kafin su fara siyan mai daga matatar Fatakwal wadda ke karkashin kulawar NNPC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here