An bude kasuwar Birnin Gwari bayan shafe kusan shekara 10 a rufe

0
89
Uba Sani

Gwamnatin jihar Kaduna ta sake bude kasuwar birnin Gwari, bayan an shafe akalla Shekaru 10, ba tare da bude kasuwar ba, saboda sha’anin tsaro.

Gwamnan jihar Uba Sani, ne ya bude kasuwar tare da karbar wasu yan ta’adda da suka tuba suka zubar da makaman su don zaman lafiya.

Uba Sani, ya ce gwamnatin jihar Kaduna tare da haÉ—in gwiwar wasu É“angarorin gwamnatin tarayya, ne suka samar da
wani kwamitin wanzar da zaman lafiya ta hanyar tattaunawa, domin samar da zaman lafiya mai É—aurewa a yankin.

Yace saboda haka a yanzu manyan yan ta’adda da mayakan su sun rungumi zaman lafiya, yana mai cewa an fara shirin yiwa tsaffin mayakan bitar gyara halayen su don cigaba da sabuwar rayuwa mai inganci.

Uba Sani, yace jami’an tsaro zasu cigaba da yakar duk mayakan da suka ki rungumar zaman lafiya, don kawo karshen su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here