Fiye da mutane 200 sun nutse a hatsarin jirgin ruwan a Niger

0
83

A jihar Niger wani mummunan hadarin jirgin kwale-kwale, ya faru a safiyar yau juma’a.

Hatsarin ya faru a yankin Dambo-Ebuchi dake kogin Niger, kuma mutane da dama ne suka rasa rayukan su.

A cewar wani da abin ya faru a gaban idon yace kwale-kwalen mallakin wani mutum ne mai suna Musa Dangana, Kuma ya dauko mutane fiye da 200, mafi yawancin su mata ne yan kasuwa da manoma, masu kokarin zuwa cin kasuwar Katcha, dake ci mako bayan mako a jihar ta Niger.

Wannan iftila’i ya sanya daukacin mutanen dake cikin jirgin kwale-kwalen sun kife a ruwa, a yayin da aka fara aikin ceto mutanen da suka gamu da hatsarin, da a yanzu aka bayar da rahoton tsamo gawar mutane 8.

Jihar Niger dai tayi kaurin suna wajen fuskantar asarar rayuwar al’umma saboda yawaitar hatsarin jirgin kwale-kwalen.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here