Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya amince da naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikatan jihar.
Cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya ce amincewar ta Æ™unshi sake fasalin albashin ma’aikatan jihar ciki har da ma’aikatan hukumomi.
Dikko Radda ya ce sabon albashin zai fara aiki daga watan Disamba mai kamawa.
Gwamnan ya yi amfani da karin albashin wajen godewa ma’aikatan jihar tare da neman su kara jajircewa a aikin su da kuma rikon amana.
A ranar Juma’a ne Æ™ungiyar NLC ta yi barazanar fara yajin aiki a wasu jihohin ranar daga ranao Litinin, saboda rashin amincewa da sabon tsarin albashi.