Tinubu zai wuce Afrika ta Kudu daga Faransa

0
54

Shugaban Nigeria Tinubu, zai wuce kasar Afrika ta Kudu daga ziyarar da yakai Faransa.

Ana kyautata zaton cewa Tinubu, zai bar Faransa, a gobe litinin tare da sauka a kasar Afrika ta Kudu.

Wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaban Bayo Onanuga ya fitar ta ce Tinubu zai zarce Afirka ta Kudu domin jagorantar taron Hukumar Ƙasashen Biyu ta BNC karo na 11 tare da Shugaba Cyril Ramaphosa.

Gabanin taron da zai gudana a ranar Talata, 3 ga watan Disamba, Tinubu da Ramaphosa za su halarci taron ministoci da zai gudana a ranar Litinin a Zauren Majalisar Tarayyar Afirka ta Kudu da ke Cape Town.

Shugabannin za su tattauna kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi dangartakar ƙasashen biyu da suka haɗa siyasa, kasuwanci, tsaro, baƙin haure, haƙar ma’adanan ƙasa, jakadanci, cinikayya da sauransu.

Onanuga ya ce tun a ranar 20 ga watan Yunin 2024, shugabannin biyu suka yi shiryawa taron a birnin Johannesburg.

A shekarar 1999 ce aka ƙirƙiri Hukumar Ƙasashen Nigeria da Africa ta kudu domin inganta alaƙar da ke tsakanin su, inda taron farko tsakanin shugabannin ƙasashen biyu ya gudana a watan Oktoba na 2019 a Pretoria.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here