Babban bankin Nigeria CBN zai yiwa ma’aikatan sa 1000 ritayar dole a watan Disamba.
Wata babbar majiya ce ta sanar da cewa babban bankin na Nigeria yana nan yana yin shirin yiwa ma’aikatan nasa su fiye da 1000, ritaya kafin karewar wannan shekara ta 2024.
:::Zamu yaki kudirin dokar harajin Tinubu a majalisa—Tambuwal
Matakin zai sanya a kashe sama da naira biliyan 50, wajen biyan ma’aikatan hakkin su na sallama daga aiki, tun da ba korar su za’a yi ba.
Wata majiya a bankin ta bayyana cewa mutum daya zai samu kudin kammala aiki wato garatuti har Naira miliyan 92, bayan aikin shekara huÉ—u a bankin.
Gwamnan bankin Olayemi Cardoso, ne ya jagoranci shirin rage ma’aikatan don sake fasalin tsarin tafiyar da aikin bankin.
A cikin watanni 10 da suka gabata, babban bankin na CBN ya sallami ma’aikata da dama, ciki har da daraktoci 17 wanda suka yi aiki lokacin tsohon gwamnan bankin Godwin Emefiele, kuma har yanzu ba a maye gurbinsu ba.
Wata takardar da CBN ya fitar, ta bayyana cewa Æ™ofar yin ritaya kafin lokacin kammala aiki a buÉ—e take ga ma’aikatan sa zuwa ranar 31 ga watan Disamban da muke ciki, kuma sanarwar tace ko a wanne matakin aiki mutum yake zai iya ajiye aikin nasa.
Sai dai damar ba ta shafi ma’aikatan da har yanzu ba a tabbatar da su ba ko kuma ba su wuce shekara guda da fara aiki ba.
Wasu jami’an CBN sun bayyana cewa aƙalla ma’aikata 860 ne suka nemi takardar neman ajiye aikin a yanzu.
Wani ma’aikaci ya bayyana cewa waÉ—anda ake sa ran za’a yiwa ritayar suna kan matakin manajoji, musamman wadanda suka yi aiki lokacin tsohon gwamnan bankin, Godwin Emefiele.
Sai dai kawo yanzu ba’a ji wata sanarwa daga CBN ba sakamakon an nemi jin ta bakin daraktar Sadarwa ta CBN, Hakama Sidi Ali, amma hakan bai samu ba.