Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, yace in aka amince da dokar haraji wasu jihohi yan kadan ne zasu ci gajiyar dokar wadda shugaba Tinubu, da majalisun dokokin kasa ke son kakabawa al’umma.
:::Yau ce ranar fara yin rigakafin cutar zazzabin cizon sauro a Nigeria.
Zulum, yace tun da farko gwamnonin arewa sun nemi shugaban kasa Tinubu, ya dakata kafin aikewa majalisa kudirin dokar don sake yin nazari akan ta da kuma yin gyara a wajen da ya dace, musamman inda za’a cutar da arewa a cikin dokar.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da gidan Talabijin na Channels ranar Lahadin da ta gabata, ya ce ƙungiyar gwamnonin Arewa na buƙatar lokaci domin tuntuɓa da kuma nazarin ɓangarorin da dokar harajin ta tanada, inda yace akwai abubuwan da har yanzu gwamnonin sun gaza fahimtar su wanda a haka ake son tabbatar da dokar ba tare da an bari an san me ta kunsa ba.
Yace a binciken da aka gudanar jihohin Lagos da Rivers, ne kadai zasu amfani gyaran dokar da kuma tara kudaden shiga masu yawa.
Zulum ya yi bayanin cewa idan har dokar ta sami amincewar Majalisar Dokoki ta kasa, za a cutar da jihohi da dama domin jihar Legas ce kaÉ—ai za ta ci gajiyar wannan manufa.