Sanata Barau I. Jibril, ya dauke daurin auren yar sa daga Kano zuwa Abuja

0
47

Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya ne aka fitar da sanarwar cewa Barau, ya yanke shawarar daura auren yar sa a fadar Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero.

Ana kyautata zaton cewa batun sauya fasalin dokar haraji ta Tinubu, da taja hankalin al’umma na daga cikin dalilin dauke daurin auren daga Kano zuwa Abuja, saboda wasu suna zaton an hada kai da Barau, wajen ganin majalisar dattawa ta amince da kudirin dokar wanda ake cewa zai cutar da arewa.

Haka zalika anyi hasashen cewa mutanen gari ka iya kawo cikas ko yin jifa ga manyan bakin da zasu zo daurin auren in aka yi a jihar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here