Mai martaba sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, ya muslintar da maguzawa 150 a karamar hukumar Takai ta jihar Kano.
- Sarkin ya bawa mutanen 150, kalmar shahada a wajen buÉ—e sabon Masallacin Juma’a da Makarantar Islamiyya da Gidauniyar Ganduje, ta gina a garin Takai, inda ya bayyana musu cewa yanzu basu da maraba da sauran al’ummar musulmai dake fadin duniya.
:::Bankin CBN zai yiwa ma’aikata 1000 ritayar dole a watan Disamba
- Ya kuma gargaÉ—e su kan yin sallah, bayar da zakkah, yin Azumin watan Ramadan, sannan su yi aikin Hajji idan Allah Ya ba su iko, saboda wadannan abubuwa sune shika-shikan addinin.
- Sarkin, ya kuma roƙi gidauniyar Ganduje, da ta samar da malamai da za su koyar da wadanda aka muslintar din yadda za su yi ibada.
- Aminu Ado, ya yaba wa ƙoƙarin kwamitin Da’awa na gidauniyar Ganduje, kan ayyukansu na yaɗa Addinin Musulunci a lungu da saƙo na Jihar Kano da wasu jihohi.
- Babban Sakataren yaɗa labarai na sarkin, Abubakar Balarabe Ƙofar Na’isa, ya ce wannan abu ya ƙara ɗaukaka darajar Addinin Musulunci a Kano.