Zamu yaki kudirin dokar harajin Tinubu a majalisa—Tambuwal

0
44

Tsohon gwamnan jihar Sokoto Sanata Aminu Waziri Tambuwal, yace zasu tabbatar da cewa majalisa bata amince da kudirin yin gyara a dokar haraji ta Nigeria ba, wadda tuni majalisar ta yiwa kudirin dokar karatu na biyu.

:::Jihohin Lagos da Rivers ne zasu amfani sabuwar dokar Haraji—Zulum

Tambuwal wanda ke wakiltar Sakkwato ta Kudu a majalisar dattawa ya bayyana cewar dokokin da gwamnatin tarayya a karkashin jagorancin shugaba Bola Tinubu ke son kakabawa jama’a ba su dace ba, don haka ba za su goyi bayan su ba.

Tsohon Gwamnan kuma jagoran jam’iyyar PDP a Sakkwato ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a karamar hukumar Shagari a yayin da yake kaddamar da tallafi ga wadanda ambaliyar ruwa da hare haren ta’addanci ya shafa.

A cewar sa al’umma sun zabe su don su kare su daga dokoki masu cutarwa kuma zasu yi kokarin ganin wannan doka bata samu amincewar majalisa ba

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here