Babu gaskiya a zaton cutar da arewa a dokar haraji—Fadar Shugaban kasa

0
39
Tinubu
Tinubu

Fadar shugaban Nigeria Bola Tinubu, ta karyata zargin da ake yi cewa dokar harajin da shugaban kasar ke son kakabawa yan kasa zata cutar da arewa, tare da cewa shima zargin fifita jihohin Lagos da Rivers a kunshin dokar ba gaskiya bane.

:::Majalisar dokikin Kano tayi watsi da dokar harajin shugaba Tinubu

Mai magana da yawun shugaban kasar Bayo Onanuga, cikin wata sanarwar daya fitar a jiya litinin yace an samar da dokar don karfafa nagartar yan Nigeria baki baki, da kuma habbaka kasuwanci, bawai cutar da wani yankin ba.

Bayanin na Onanuga, ya kasance tamkar mayar da martani ga kalaman gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum, wanda yace yana kalubalantar dokar saboda a cewar sa an samar da ita domin inganta jihohin Lagos da Rivers da kuma manufar dakile jihohin arewa.

Mai magana da yawun shugaban yace irin wadannan kalamai basu da sahihanci.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here