Gwamnatin Kano tace mutane sun ki siyan kujerun aikin hajjin shekarar 2025

0
54

Gwamnatin Kano ta bayyana damuwa akan cewa an samu karancin masu sayen kujerun aikin hajji don sauke farali a shekarar 2025.

Shugaban hukumar alhazai ta jihar Kano, Alhaji Lamin Rabi’u Danbappa, ne ya bayyana damuwar a yau talata, lokacin da hukumar ta gabatar da wani taron wakilanta dake daukacin kananun hukumomin jihar 44.

:::Kotu ta kwace gidaje 753 a wajen tsohon jami’in gwamnati bisa zargin almundahana

Wata sanarwa da kakakin hukumar Sulaiman A. Dederi ya fitar ta ce shugaban ya bayyana hakan ne yayin wani taron haÉ—in gwiwa tsakanin ma’aikatan hukumar manyan jami’anta na Æ™ananan hukumomin Kano 44 a ofishin hukumar.

Lamin, yace dole ne wakilan hukumar jin dadin alhazai dake kananun hukumomi su tashi tsaye domin lalubo hanyar da za’a siyar da adadin kujerun aikin hajjin da aka bawa Kano.

Hukumar alhazan ta sanya ranar 1 ga watan Janairu na shekara mai kamawa, 2025, a matsayin ranar rufe karɓar kuɗin ajiya na aikin Hajjin na bana daga maniyyata a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here