CBN zai hukunta bankunan da basa saka kudi a ATM

0
21

Babban bankin kasa CBN yace zai dauki mataki akan bankunan kasuwancin dake kawo cikas ga tsarin inganta zagayawar takardun kudi a hannun jama’a, musamman wadanda ke kin saka kudi a na’urar ATM.

CBN yace zai bayar da lambobin waya da adireshin aikewa da sako don mutane su bashi rahoton duk wani bankin daya basu ma’atsalar karbar kudi don daukar matakin daya dace.

:::Yan kasuwar Kano sun yi alkunut saboda rashin wutar lantarki

Babban bankin na Nigeria yace inganta zagayawar kudi daga banki zuwa mutane zai kara gyara alakar bankunan da abokan huldar su.

Bankin CBN, ya sanar da hakan tun a ranar 29, ga watan Nuwamban daya gabata, yana mai cewa matakin daya dauka zai taka burka akan karancin kudin da ake fuskanta a hannun mutane.

Duk wani mai yawan cirar kudi a bankuna da ATM ya kwan da sanin kalubalen dake tattare da zuwa neman tsabar kudi a bankunan kasuwancin kasar nan, wanda ake fama da karancin kudin tun kusan watanni 5 da suka shude.

Za’a iya cewa tun lokacin da tsohon shugaban Nigeria Buhari, ya kaddamar da shirin sauya fasalin takardun kudi na 1000, 500, da 200, mutane ke samun karancin kudi a hannu.

Haka zalika akwai batun cewa in har mutu ya dauki wani adadin tsabar kudi daga banki ba zai kara cirar kudi ba sai bayan mako guda.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here