Majalisar dattawa ta datakar da tattaunawa akan dokar harajin Tinubu

0
50

Bayan yiwa kudirin sauya fasalin karbar haraji na kasa karatu na biya majalisar dattawa ta jingine tattaunawa akan kudirin dokar harajin.

Majalisar ta sanar da dakatar da cigaba da tattaunawa akan kudirin, lokacin zaman ta na yau laraba a zauren majalisar dake birnin Abuja.

Jingine tattaunawar yazo jim kadan bayan gwamnatin tarayya ta nemi ma’aikatar shari’a tayi aiki da majalisar wajen samun daidaito a fannonin kudirin da ake ganin akwai cuta a ciki.

A halin da ake ciki Majalisar ta umarci kwamitin da ta miÆ™a wa Æ™udurin ya dakatar da nazari a kansa, yayin da aka kafa wani kwamiti wanda zai yi aiki tare da ma’aikatar shari’a domin duba É“angarorin Æ™udurin da ake taÆ™addama a kai.

Shi dai wannan kudirin dokar haraji ya zamo babban abin tattaunawa a tsakanin yan Nigeria, wanda wasu ke zargin an yi rufa-rufe, cikin kudirin tare da zargin akwai sadarorin da bai kamata a yi amfani dasu cikin dokar ba.

Hakan ya haifar da zazzafar mahawara tun daga kan yan majalisar har kawo sauran yan kasa da masana tattalin arziki.

Tuni dai majalisar tattalin arzikin kasa ta nemi a dakatar da dokar, sannan gwamnonin arewa ma sun roki a yi wasti da ita, sai dai shugaban Nigeria Tinubu, ya dage akan bakan sa na samar da sabuwar dokar harajin, inda fadar shugaban tace ana son kafa dokar ce don inganta walwalar mutanen Nigeria, sabanin zargin da ake yi na cewa zata cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here