Tuni dai kotu ta kwace gidajen, da kuma mika su ga gwamnatin tarayya.
Hukumar EFCC, ce ta shigar da Emefiele, kara bisa zargin sa da almundahana da wawure dukiyar gwamnati.
Tun bayan cire Emefiele daga mukamin gwamnan babban bankin, gwamnatin Nigeria ke binciken sa karkashin jagorancin hukumar EFCC, mai yaki da cin hanci da rashawa.