Gwamnatin Kano zata cigaba da karbar haraji a wajen matuka babur mai kafa uku

0
73

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin ta na dawo da karbar haraji daga hannun matuka babura masu kafa uku.

Kwamishinan Sufuri na Jihar Muhammad Ibrahim Diggol, ne ya bayyana hakan, yayin tattaunawarsa da Kafar yada Labarai ta Hikima Radio, a shirin su mai suna Hannu Daya.

Tun a kwanakin baya Gwamnatin jihar Kano ta yanzu karkashin Abba Kabir Yusuf, ta sanar da cewa zata dawo karbar harajin, amma abin ya lafa sakamakon wasu dalilai.

Tsohon gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ne ya kirkiro karbar haraji daga hannun masu haya da babura masu kafa uku.

A lokacin da ake karbar harajin an rika samun sabani tsakanin masu baburan da jami’an hukumar kula da cunkoson ababen hawa ta Kano, KAROTA wanda sune masu alhakin tabbatar da biyan harajin.

Lokacin karbar harajin kowanne Matukin babur mai kafa uku yana biyan naira 100, a kowacce rana in har ya fito aiki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here