Gwamnatin Kano zata fara karbar haraji daga ma’aikatar lafiya ta jihar

0
51
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnatin jihar Kano ta sanar da shirin ta na fara karbar haraji daga ma’aikatar lafiya ta jihar.

Kwamishinan lafiya na jihar Dr. Abubakar Labaran Yusuf, ne ya sanar da hakan a yau bayan ya kammala kare kasafin kudin ma’aikatar sa na shekarar 2025, a zauren majalisar dokokin Kano.

A cewar sa ma’aikatar zata tattara harajin ne daga asibitocin jihar, wanda hakan zai fara aiki daga shekara mai kamawa.

Ya kara da cewa sun fahimci akwai bangarorin da za’a iya samarwa gwamnati kudaden shiga a fannin asibitocin.

Matsin tattalin arziki da ake fuskanta dai na daga cikin dalilin da yasa gwamnatoci nemo hanyoyin da zasu kara samun kudaden shiga, yayin da al’umma ke kokawa akan tsadar rayuwa, musamman saboda wasu manufofin gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here