Rundunar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana cewa ta gano cewa mayakan Lakurawa ne suka dasa nakiyar da wata motar haya ta taka a hanyar zuwa zarin da sadau na karamar hukumar Maru, har mutane 6, suka rasa ransu.
Kwamishinan Yan sandan Jihar Muhammad Dalijan, ne ya sanar da hakan a yau, lokacin da ake zantawa dashi a kafar talbijin ta Channels a cikin shirin su na hantsi.
:::Majalisar dokokin Kano zata yi doka akan masu siyar da Gas din girki a cikin al’umma
Idan za’a iya tunawa a jiya mun baku labarin yadda wasu matafiya suka rasu sannan wasu suka jikkata biyo bayan taka wata nakiya da ake kyautata zaton yan fashin daji ne suka dasa ta akan hanya don ta hallaka matafiya.
Jaridar Punch, ta rawaito cewa akalla mutane 6, ne suka mutu yayin da 8, suka ji munanan raunika, lokacin motar tasu ta taka nakiyar a hanyar zuwa kauyen dan sadau, na karamar hukumar Maru dake Zamfara.
Motar data taka nakiyar ta kasance ta haya ce kirar Golf, wadda fashewar nakiyar ta yi raga-raga da ita yanda ba zata moru ba.
Wannan shi ne karo na biyu da ake zargin ‘yan fashin suna dasa irin wannan nakiyar a mako guda, sakamakon a ranar Lahadin da ta gabata, maharan sun dasa wata nakiya a garin Maru da ke jihar ta Zamfara, da wata motar haya ta taka, kuma ta yi sanadiyyar mutuwar mutum daya
Jihar Zamfara na daya daga cikin jihohin arewa maso yamma masu fama da kalubalen rashin tsaro musamman ayyukan yan fashin daji masu garkuwa da mutane da kuma kisa babu dalili.