Tsaffin sojojin Nigeria sun yi zanga-zangar neman hakkin su a wajen gwamnati

0
58

Tsaffin sojojin Nigeria, masu yawan gaske sun yi zanga-zangar neman hakkin su a wajen gwamnatin tarayya, inda suka mamaye ofishin ma’aikatar kudi ta tarayya tare da rufe hanyar shiga shalkwatar ma’aikatar a safiyar yau Alhamis.

Tsaffin jami’an da suka mamaye ma’aikatar kudin sun zauna a ofishin tun misalin karfe 7:30, na safiya wanda suka je wajen tare da kayan kwanciya bacci, sun kuma ce gwamnatin ta gaza biyan su karin kaso 20 zuwa 30 a cikin dari da akayi musu a cikin hakkin su tun daga Junairun 2024 zuwa Nuwamba.

:::Lakurawa ne suka dasa nakiyar data kashe matafiya a Zamfara—Yan Sanda

Wannan zanga-zanga tazo awanni 12, bayan da wasu tsaffin sojojin suka gudanar tattaki don neman a biya su kudaden fanshon su da sauran hakkokin da suka ce gwamnati ta rike musu.

Daya daga cikin tsofaffin sojojin mai suna Innocent Azubuike, yace kin biyan su hakkin nasu ya kara jefa su kuncin rayuwa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here