A karon farko bayan watanni 9, darajar Ethereum Coin, daya ta sake zarta Dala dubu 4, sakamakon yadda kasuwar kudin crypto ke samun tagomashi tun bayan samun nasarar Donald Trump, daya lashe zaben shugaban kasar Amurka.
A yau juma’a 6/12/24, darajar Ethereum daya takai Dala 4,029, kwatankwacin naira 6,768,720, a kudin Nigeria.
Kudin crypto, na Ethereum, shine mafi karfi a kasuwa bayan Bitcoin, wanda shine jigon kasuwar crypto.
Ana hasashen manyan masu zuba hannun jari a kasuwancin Crypto zasu cigaba da zuba kudi a fannin da hakan zai kai kasuwar wani mataki da ake cewa Bull Run, da masu harkar crypto ke samun makudan kudade.
A jiya alhamis, ne darajar kowanne Bitcoin daya ta zarce Dala dubu dari, a karon farko cikin tarihin kasuwar crypto.
Ana kyautata zaton cewa zuwa watan Junairu na shekarar 2025, darajar Bitcoin zata iya kusa kaiwa Dala dubu 150.