Kamfanin Turkiyya zai inganta harkokin noma a Zamfara

0
60

Gwamnatin jihar Zamfara ta hada hannu da wani kamfanin kasar Turkiyya don habbaka harkokin noma.

Kamfanin Direkci, shine zai yi kokarin samar da lambu na zamani da sauran kayan zamani na noma wanda zasu saukaka noma da aikin gona a jihar.

A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne, Nurullah Mehmet, Manajan Darakta kuma Babban Jami’in Gudanarwa na cibiyar Direkci, ya jagoranci tawagar da suka kai wa Gwamna Dauda Lawal ziyarar aiki a ofishinsa a gidan gwamnati da ke Gusau.

Kamfanin na ƙasar Turkiyya na shirin kawo sauyi a harkar noman Zamfara ta hanyar noman auduga, da raƙe, da waken suya.

Baya ga noman gargajiya, cibiyar za ta bullo da hanyoyin noma na zamani, gami da amfani da fasaha wajen samar da lambuna da kiwon kaji, waɗanda za su ƙara inganta fannoni da dama a jihar.

A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya jaddada ƙudirin gwamnatin sa na tabbatar da samar da abinci da samar da ayyukan yi ga al’ummar Jihar Zamfara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here