Jihohin Kano da Katsina, sun zama sahun gaba wajen matsalar rashin isassun takardun kudi a hannun mutane da hakan ya faro tun daga bankuna zuwa kan masu POS da ake samun kudin a wajen su.
Wani bincike ya nuna cewa a yanzu haka mafi yawancin jihohin Nigeria na fama da karancin takardun kudi sai dai abun ya ta’azara a Kano da Katsina.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa bankuna basa bayar da tsabar Kudin daya wuce naira dubu ashirin ga mutum daya a kowacce rana.
Yayin da masu Sana’ar POS ke cajar naira 200 akan kowacce dubu 10 da suka bawa mutum sabanin naira 100 da suka saba karba a baya.
Hakan ya fara yin tasiri ga masu kananun sana’o’i da kuma yankin karkara da wasu mutanen karkarar basa yin amfani da bankuna.
Wata matsalar bayan karancin takardun kudi itace idan aka tashi tura kudi daga asusu zuwa wani asusun shima yakan bayar da da matsalar kudin yaki zuwa da wuri.
A makon daya gabata ne aka jiyo mataimakin shugaban Nigeria Kashim Shettima, na cewa bankuna su kawo karshen matsalar karancin tsabar Kudin.