Sai an fara binciken manya za’a yi nasara a yaki da cin hanci—Obasanjo

0
36

Tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo, yace fara binciken manya akan aikata laifin cin hanci da rashawa itace kadai hanyar da za’a bi a magance matsalar cin hanci a kasar.

Tashar talbijin ta Channels, ta rawaito cewa Obasanjo, ya bayyana hakan a jiya lokacin da ake zantawa dashi a wani gidan Radiyo dake Abeokuta na jihar Ogun.

Tsohon shugaban ya kuma nemi a samar da canji dangane da yanayin daukar aiki da nada mutane akan mukaman Gwamnati.

A cewar sa yakar cin hanci da rashawa abu ne dake bukatar cigaba ba tare da tsayawa ba da kuma nuna kaunar hakan a zukatan shugabanni.

Olusegun Obasanjo, yayi imanin cewa in har aka fara yakar cin hanci daga kan shugabannin zai zama abin sauki in aka zo kan kananun ma’aikata da sauran al’umma.

Haka zalika yace ba za’a iya magance matsalar cin hanci da rashawa a lokaci guda ba.

A mafi yawancin lokuta ana ganin cin hanci da rashawa shine makasudin abinda ya jefa Nigeria cikin tabarbarewar al’amura.

Masana na ganin cewa a kowanne fannin kasar nan cin hanci da rashawa ya samu wajen zama da hakan ke tabbatar da cewa sai anyi da gaske kafin a ci nasarar yaki da shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here