Sakataren gwamnatin tarayya George Akume, ya nemi yan siyasar arewa masu son tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027 dasu dakata har zuwa Shekarar 2031.
A cewar sa sai Shugaban Nigeria Tinubu ya kammala wa’adin mulkin sa a karo na biyu yan arewa zasu iya samun damar mulkar kasar.
Akume a hirarsa da gidan talabijin na TVC, ya ce daga kudancin Najeriya ne ya kamata a fitar da shugaban ƙasa a 2027.
Sakataren gwamnatin yace kamata yayi a Kyale Tinubu ya yi shekara 8 akan mulki har bayan kammala wa’adin mulki a karo na biyu sakamakon shi dan kudancin Nigeria ne.
Ya ƙara da cewa ya kamata a bar ƴan kudu su yi mulki na shekara takwas daga nan sai a koma arewa, sannan yace idan ba haka ba za a lalata kasar ne Kawai.