Tsohon mataimakin shugaban kasa, kuma dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar PDP a zaben shekarar 2023 Atiku Abubakar, yace yan Nigeria suke da hurumin zabar shugaba ko daga wanne yanki ya fito na kudu ko arewa a zaben shekarar 2031.
Kalaman na Atiku, sun zo a matsayin martani ga bayanan sakataren gwamnatin tarayya George Akume, da yace kamata yayi yan arewa su jingine batun tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2027, har sai Shugaban Ƙasar na yanzu Tinubu, ya kammala wa’adin mulki na biyu a shekarar 2031.
Akume, yace in yan arewa suka karbi mulkin Nigeria a kakar zabe mai zuwa hakan zai lalata tafiyar da al’amuran kasar saboda dan arewa ya mulki Nigeria tsawon shekara 8, yana mai cewa barin yan kudu suma suyi mulkin shekara 8 shine abinda ya dace.
Amman a martanin Atiku, ta hannun mai magana da yawun sa Paul Ibe, ya ayyana kalaman Akume, a matsayin rashin adalci, yana mai cewa yan kasa ne zasu yanke hukuncin wanda ya kamata ya mulke su daga kudu ko arewa, sannan yace babu saruan daga kafa tsakanin su da gwamnati mai ci a fannin neman takara.