Wani wani mummunan hatsarin mota yayi ajalin matafiya 14, a jihar Jigawa kamar yadda rundunar yan sandan jihar ta sanar ta bakin kakakin ta DSP Lawan Shisu.
:::Yan fashi da makami sun kashe kanwar Gwamnan Jihar Taraba
Shisu, yace lamarin ya faru a jiya litinin wanda ya rutsa da wata mota dake hanyar zuwa Makera ta karamar hukumar Kafin Hausa daga karamar hukumar Hadejia.
Kakakin ya tabbatarwa da BBC, cewa matukin motar ya tsira da rai sai dai yana cikin mawuyacin hali saboda raunikan daya samu.
Hatsarin ya afku bayan da motar mai kirar Golf ta fada kasan wata gada data karye a lokacin ambaliyar daminar data gabata, wanda haka yasa mutanen cikin motar 14 suka rasu.
Ya kuma bayyana cewa a halin yanzu direban, wanda ke cikin mawuyacin hali na samun kulawa a asibiti yayin da tuni wasu daga cikin ƴan’uwan waɗanda abin ya shafa suka karɓi gawarwakinsu.
Hatsarin ya rutsa ne da mata takwas, da maza magidanta biyu da kuma matasa guda huÉ—u.