Hukumar kwallon kafa ta duniya ta sahalewa kasar Saudi Arabia, damar karbar bakuncin gasar cin kafin duniya ta shekarar 2034.
Shugaban hukumar Gianni Infantino, ne ya sanar da hakan a yau bayan da hukumar FIFA, ta gudanar da wani taro akan kasashen da za’a bawa damar karbar bakuncin gasar.
Tun da farko gwamnatin kasar Saudi Arabia, ce ta nemi a bata damar karbar bakuncin gasar.