Awanni 48 bayan faruwar mummunan hadarin mota da yayi sanadiyyar mutuwar mutane 14, a jihar Jigawa, an sake fuskantar hatsarin daya kashe mutane 6.
Hatsarin na yanzu ya faru a daren jiya Talata a hanyar Auyo zuwa Adiyani, dake karamar hukumar Guri.
Wata majiya tace mamatan sun kasance dangi guda kuma yan uwan juna, da suka gamu da ajalin nasu bayan sun dawo daga gaisuwar mutuwar mutanen da suka yi hatsarin ranar lahadin data gabata wanda yayi ajalin mutane 14.
Wani shaidar gani da ido yace wannan abu ya faro lokacin da ake tsaka da jimamin mutane 14 da hatsarin farko ya hallaka.
Zuwa yanzu dai a cikin kwanaki biyu hatsarin mota yayi sanadiyyar mutuwar mutane 20 da suka fito daga yanki guda a jihar ta Jigawa, da hakan ke nuna cewa akwai bukatar kula da lafiyar hanyoyin sifurin jihar don kare rayukan al’umma.
Mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar DSP Shi’isu Lawan Adam, ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda yace suna kan gudanar da bincike akan dalilin yawaitar hatsarin mota a Jigawa cikin yan kwanakin nan.