Shugaba Tinubu ya nada sabon akanta janar na tarayya

0
45

Shugaban Nigeria Bola Tinubu, ya nada sabon akanta janar na gwamnatin tarayya biyo bayan hutun kammala aikin da akanta mai barin fadi Oluwatoyin Sakirat Madein, ta tafi.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Tinubu, Bayo Onanuga ya fitar a jiya Talata yace a yanzu shugaban kasar ya nada Shamseldeen Babatunde Ogunjimi a matsayin mukaddashin Akanta Janar na kasa, kuma nadin nasa ya fara aiki nan take.

Shamseldeen Babatunde, ya kasance babban darakta a ofishin Akanta Janar na Tarayya, sannan yana da kwarewa ta fiye da shekaru 30 a bangaren tafiyar da kudade a ma’aikatun gwamnati da masu zaman kansu.

Ya rike manyan mukamai da suka hada da Daraktan kudi a ofishin Akanta Janar na kasa .

Shugaba Tinubu ya yabawa Akanta Janar ta Tarayya mai barin gado, bisa sadaukarwar da ta yi ga kasa.

Bayan ta kai shekarun yin ritaya a aikin gwamnati, Dr. Madein za ta yi ritaya daga ranar 7 ga watan Maris, 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here