INEC ta karyata labarin rasuwar shugaban ta na kasa

0
36

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta yi watsi da jita jitar da aka fara yada cewa shugaban ta na kasa Farfesa Mahmud Yakubu, ya rasu.

Jami’in yada labarai na Hukumar Rotimi Oyekanmi, ya ce labarin kanzon kurege ne da bashi da tushe ballantana makamai.

INEC tace babu gaskiya a bayanan da aka rika yadawa a kafafen sada zumunta masu bayyana mutuwar Farfesa Mahmud Yakubu, a wani asibitin kasar Burtaniya.

Sanarwar ta ce mutane su yi watsi da labarin mutuwar shugaban na INEC, inda ta ce yana cikin koshin lafiya, kuma bai ma yi wata tafiya zuwa birnin Landan ba a cikin shekaru biyu da suka wuce.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here