An gurfanar da wata mata mai shekaru 30 da ake zargin ta hallaka yar jaririyarta mai watanni 8 da maganin Bera.
Rundunar tsaron al’umma ta farin kaya Civil Defence, ce ta gurfanar da matar a kotun Majistare dake Kafanchan ta jihar Kaduna.
Mai gabatar da ƙara, Marcus Audu, ya shaida wa kotu cewa wani mai suna Godfrey Sunday daga unguwar Fadia Bakut, Zonkwa ne ya kai rahoton lamarin ofishin NSCDC a ranar 11 ga Disamba da muke ciki.
A cewar Audu, a ranar 10 ga Disamba, wacce ake zargi ta shayar da ’yarta da maganin bera don halaka yar ta, wanda bayan bata maganin aka kaita asibiti inda aka tabbatar da rasuwar jaririyar bayan kwana daya a asibitin Zonkwa.
Mai gabatar da kara ya ce wacce ake zargi ta amsa laifin da ake tuhumar ta da aikatawa yayin gudanar da binciken.
An ɗage shari’ar zuwa ranar 17 ga Disamba domin ci gaba da sauraro