Sojojin Nigeria masu atisayen Fansan Yamma, sun samu nasarar lalata sansanin mayakan Lakurawa 22 a jihar Sokoto, tare da kashe mayakan masu yawa.
Sojojin sun kuma bankado manyan makamai tare da alburusai a yayin farmakin da suka kaiwa yan ta’addan.
Mai rikon mukamin babban jami’in runduna ta 8 Burgediya Janar Ibikunle Ajose, ne ya sanar da hakan a jiya lokacin da yake jawabi ga sabuwar tawagar da aka samar a yankin jihohin Kebbi da Sokoto, don fatattakar mayakan Lakurawa.
Ibikunle, yace sakamakon dakarun Fansan Yamma, a yanzu haka ana cigaba da samun nasarar yakar ayyukan ta’addanci a jihohin Kebbi da Sokoto.