Gwamnan Kano yayi sabbin nade-naden mukamai

0
38

Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da yin wasu sabbin nade-naden mukamai a hukumonin jihar, tare da canjawa wasu shugabannin wurin aiki.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a yau lahadi.

Sabbin nade-naden mukaman sun hadar da;
1. Dr. Ibrahim Musa, a matsayin mai bawa Gwamnan shawara a fannin ayyukan lafiya.

2. Dr. Hadiza Lawan Ahmad, mai taimakawa gwamnan a fannin zuba jari da hukumomi masu zaman kansu.

3. Sani Musa Danja, mai taimakawa gwamnan a fannin matasa da wasanni.

4. Barr. Aminu Hussain, mai bawa Gwamnan shawara a fannin shari’a.

5. Dr. Ismail Lawan Suleiman, mai bawa Gwamnan shawara a fannin yawan al’umma.

6. Nasiru Isa Jarma, mai bawa Gwamnan shawara a fannin kungiyoyi masu zaman kansu.

7. Hon. Wada Ibrahim Daho, a matsayin kwamishinan hukumar bayar da Ilimin bai daya.

8. Hon. Ado Danjummai Wudil, shugaban Hukumar Gudanarwa da Nasiha.

9. Dr. Binta Abubakar, shugabar hukumar Ilimin manya.

10. Hon. Abubakar Ahmad Bichi, shugaban hukumar tallafawa masu ciniki akan tituna.

11. Hon. Abdullahi Yaryasa, mamba a hukumar kula da ayyukan majalisa.

12. Dr. Yusuf Ya’u Gambo, shugaban hukumar tsare tsaren ayyukan gwamnati.

Daga cikin wadanda aka sauyawa wajen aiki sun hadar da;

1. Hon. Kabiru Getso Haruna, shugaban hukumar bayar da tallafin karatu.

2. Hon. Rabi’u Saleh Gwarzo, shugaban hukumar kula da manyan makarantun sakandire.

3. Dr. Kabiru Ado Zakirai, shugaban fannin kula da guraren karatu na jihar Kano (Library)

4. Dr. Abubakar Musa Yakubu, shugaban Asibitin Gidan gwamnati.

5. Yusuf Jibrin Oyoyo, mai bawa Gwamnan shawara akan harkokin dalibai.

6. Hon. Isa Musa Kumurya, mai bawa Gwamnan shawara a fannin kungiyoyin tsaro.

7. Hajia Fatima Abubakar Amneef, mai bawa Gwamnan shawara a fannin wayar da kan al’umma.

8. Comrade Nura Iro Ma’aji, mai bawa Gwamnan shawara a fannin samar da ayyukan yi.

Sanarwar ta bayyana cewa nadin mukaman sun fara aiki nan take.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here