Tsohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnan Kano, Alhaji Shehu Wada Sagagi, ya yi jawabai da suka danganci cire shi daga mukamin sa da gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, yayi a ranar Alhamis data gabata.
Wada Sagagi, ya bayyana cewa tun farko a shirye yake wajen karbar kowacce irin kaddarar data zo masa a rayuwa.
Sagagi, ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da wani shirin siyasa da al’amuran yau da kullum, da ake sakawa a shafukan sada zumunta Wanda Yakubu Musa Fagge, ke jagoranta.
Sagagi, ya mika godiyar sa, ga Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, daya bashi dama a cikin gwamnatin sa tun a ranar farko da aka rantsar da shi a matsayin gwamna.
Koda aka tambaye shi ko cire shi daga mukamin shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin Kano zai raba shi da gwamnatin Kano cewa yayi har yanzu shi cikakken dan jam’iyyar NNPP ne kuma mai goyon baya da yiwa gwamna Abba, biyayya.
Sannan yace zai cigaba da yin biyayya ga tsarin kwankwasiyya, yana mai cewa ya koyi abubuwan alkairi da ilimi mai yawa a tafiyar da yayi da Gwamnan Kano.
Sagagi ya Kuma bayyana cewa akwai kauna mai kyau tsakanin su da Abba Kabir Yusuf, sannan yayi watsi da bayanan da aka yada na cewa anyi amfani da zigar mutane wajen cire su daga mukaman.
Shehu Wada Sagagi, yace da Gwamna Abba Kabir Yusuf, yana amincewa da zancen da mutane suke kawo masa da tun tuni an cire Sagagin daga mukamin.
Sagagi, ya Kuma bayyana cewa duk masu bayyana wasu abubuwan rashin dadi akan sa zasu fuskanci hukunci a Wajen mahaliccin su.
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, dai ya cire wasu daga cikin yan majalisar zartarwar sa cikin su harda sakataren gwamnatin Dr Abdullahi Baffa Bichi, da karin wasu kwamishinoni a matsayin garambawul.
Amma Sagagi ya ce duk wadanda aka cire ba wani laifi suka yi ba, lokacin da Allah ya daukar musu na shugabanci ne ya kare.