An yankewa yan ta’adda 200 hukuncin kisa

0
51

Kimanin yan ta’addan kasar nan da masu daukar nauyin su 200 aka yankewa hukuncin kisa ko kuma daurin rai da rai a gidan yari.

An samu mutanen ne cikin mutum 500 da aka gurfanar a manyan kotun kasa, bisa zargin alaka da ayyukan ta’addanci.

Ofishin Mashawarcin Shugaban Ƙasa kan Sha’anin Tsaro ne ya gurfanar da su a cibiyar da ake tsare da su a yankin Kainji da ke Jihar Neja.

Ofishin ya bayyana cewa daga cikin mutanen akwai waɗanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin shekara 20 zuwa shekaru 70, gwargwadon girman laifin da aka same su da shi.

Da yake bayani kan kammala shari’ar rukuni na 6 na waɗanda ake zargin, Ofishin ya bayyana cewa daga ranar 9 zuwa 13 ga watan Disamban nan da muke ciki, an gurfanar mutum 237 da ake tsare da su a cibiyar.

Ofishin ya sanar a ranar Lahadi cewa waɗanda aka yanke wa hukunci mafi tsanani su ne waɗanda aka kama da laifin yi wa mutane yankan rago da garkuwa da mutane a yankin Gina Kara Kai da ke Jihar Borno.

Suran su ne waɗanda aka samu da laifin kai wa mata da ƙananan yara hari da kuma lalata wuraren ibada.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here