Gwamnan Kano ya aikewa majalisa sunayen kwamishinoni 6 ciki har da Sagagi

0
45
Abba Gida-Gida
Abba Gida-Gida

Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya aikewa majalisar dokokin jihar sunayen mutane 6 da yake son nadawa a matsayin kwamishinoni.

Gwamnan ya aike da Sunayen don neman sahalewa daga majalisar.
Kakakin majalisar Ismail Falgore, ne ya sanar da hakan a zaman majalisar na yau litinin.

Mutanen sun hadar da;

1- Alh. Shehu Wada Sagagi
2- Alh. Abdulkadir Abdulsalam (AG)
3- Ibrahim A. Waiya
4- Dr. Isma’il Danmaraya
5- Dr Ghaddafi Sani Shehu
6- Dr. Dahir M. Hashim.

A yanzu haka akwai ma’aikatu 6 a jihar Kano, wadanda babu kwamishina a cikin su sakamakon garambawul da Gwamnan ya gudanar a ranar alhamis data gabata.

Ma’aikatun sun kunshi ta Raya karkara, ma’aikatar kudi, Ma’aikatar yada labarai, ma’aikatar muhalli, Ma’aikatar jinkai, da ma’aikatar lantarki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here