Gwamnatin tarayya ta bayar da umarnin hawa jirgin kasa kyauta har zuwa sabuwar shekarar 2025

0
40

Gwamnatin ta sanar da cire kudin tikitin jirgin kasa ga kowa daga ranar 20 ga Disamba zuwa 6 ga Junairu, don saukakawa mutane a lokacin kirsimeti da sabuwar shekara.

Haka zalika gwamnatin tarayyar ta canjawa jami’ar birnin tarayya Abuja suna zuwa sunan tsohon shugaban kasa na mulkin soji wato Yakubu Gowon.

Ministan yada labarai Muhammad Idris, ne ya bayyana hakan a yau bayan kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya da Tinubu, ya jagoranta, a yau.

Ministan ya kuma sanar da cewa majalisar zartarwa ta tarayya zata tafi hutu daga ranar 18 ga Disaba zuwa 6 ga Junairun 2025.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here