A yanzu haka shugaban Nigeria Bola Ahmed Tinubu, na jagorantar taron majalisar zartarwar tarayya da ake kyautata zaton shine na karshe da za’a gudanar a wannan shekara ta 2024, a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya Abuja.
:::Tinubu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 a ranar Laraba
Taron yana gudana ba tare da mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ba sakamakon ya halarci taron bude wata matatar man fetur a birnin Dubai, na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, da aka samar da kimanin kudade dala miliyan 315.
Shima ministan harkokin waje Yusuf Tugga, da karamar ministar sa Bianca Odumegwu-Ojukwu, basu halarci taron ba.
Wasu daga cikin mahalartan taron sun kunshi sakataren gwamnatin tarayya George Akume, sai mai bawa shugaban kasa shawara a fannin tsaro Nuhu Ribadu, da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa Gbajabiamila, da shugabar ma’aikatan tarayya Didi Walson-Jack, da sauran su.