Tinubu zai gabatar da kasafin kudin shekarar 2025 a ranar Laraba

0
38

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu, ya jingine gabatarwa da majalisun dokokin kasa kasafin kudin shekarar 2025, daga ranar talata zuwa ranar laraba 18 ga Disamba.

Jaridar Punch, ta rawaito cewa wakilinta dake majalisar dattawa ne ya samu tabbacin hakan daga wasu manyan jami’an majalisar.

:::Hauhawar farashin kayan masarufi takai kaso 34.6

Jaridar tace an sanar da ita cewa nan bada jimawa ba za’a sanar da daga lokacin gabatar da kasafin a hukumance.

A zaman majalisar na ranar alhamis data gabata ne shugaban majalisar dattawa Godswil Akpabio, yace Tinubu zai gabatar da kasafin a gobe, sai gashi an samu fitar labarin cewa sai ranar laraba zai gabatar da kasafin kudin na 2025.

A cewar Akpabio, shugaban kasar ne ya sanar da shirin sa na bayyanawa majalisun dokokin kasa kasafin a ranar 17 ga watan Disamba, wanda yace za’a gabatar da kasafin a zauren majalisar wakilai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here