Gwamnatin jihar Niger ta ayyana yawaitar tashin gobara a jihar da cewa wata babbar annoba ce.
Gwamnan jihar Neja, Umar Bago, ne ya bayyana hakan a sakon jaje zuwa ga mazauna da masu shaguna da annobar gobara ta shafa a kusa da wata tashar sufuri da ke Minna.
Gwamna Bago, yana bayyana haka ne a wata sanarwa da sakataren labaran sa, Bologi Ibrahim ya fitar, yana mai jaddada cewa Gwamnan ya jajantawa mutanen da abin ya faru da su
Gwamnatin Niger, tace Allah zai mayar wa yan kasuwar da al’umma da alkairi in suka mika lamuran su ga Allah.
Daga karshe Bago, yace zai tallafawa duk wadanda abin ya shafa.