ECOWAS zata samar da kudin kashewa na bai daya mai suna ACO

0
61

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS, ta kara jaddada aniyar ta wajen samar da kudin bai daya a tsakanin kasashen dake karkashin ta.

Kungiyar tace za’a samar da kudin tare da saka masa suna (ACO)

Ƙasashe mambobin ƙungiyar sun cimma wannan yarjejeniya a lokacin da suka gudanar da wani taro a birnin tarayyar Nigeria Abuja.

Tun a baya ECOWAS tayi yunkurin samar da kudin ACO, a cikin shekarar 2020, sai dai hakan bai samu ba sakamakon barkewar cutar coronavirus a karshen shekarar 2019.

Amma yanzu, sun yanke shawarar ƙaddamar da kuɗin a shekarar 2027, kamar yadda tashar talbijin ta Channels ta bayyana.

ECOWAS ta ce ACO zai taimaka wajen inganta harkokin kasuwanci, da tattalin arzikin ƙasashen dake karkashin ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here