An samu karuwar lallafin kudin lantarkin da gwamnati ke biyawa yan Nigeria–Hukumar NERC

0
44

Hukumar dake kayyade farashin wutar lantarki ta kasa NERC tace an samu karuwar kudaden tallafin wutar lantarkin da gwamnatin Nigeria ke biyawa al’umma zuwa naira biliyan 199.64, a cikin watan Disamba.

Wani rahoton tashar talbijin ta Channels, ya nuna cewa a watan Nuwamba gwamnatin ta biya tallafin lantarki na naira biliyan 194.26, wanda hakan ke nuni da cewa an samu karin kaso 2.76, idan aka kwatanta da abin data biya a watan Disamba.

:::Nigeria zata biya bashin naira triliyan 15 a kasafin kudin ta na triliyan 47.9

NERC tace hakan baya rasa nasaba da faduwar darajar kudin kasar nan wato naira, sannan kuma a yan kwanakin nan ba’a samu canjin farashin wutar lantarki ba.

Batun wutar lantarki a Nigeria ya kasance abin ciwa yan kasa tuwo a kwarya sakamakon rashin samun wutar da kuma fuskantar karin farashin ta akai-akai.

Ko a yan kwanakin baya kafin a samu lalacewar lantarkin arewa sai da aka kara farashin lantarkin ba tare da al’umma sun ankara ba.

Har yanzu a wasu daga cikin biranen kasar nan akwai guraren da ake gaza samun wutar lantarkin awanni 5 a kowacce rana, da hakan ke kara durkusar da masu kananun sana’o”i.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here