Wani mutu mai suna Dauda Haruna, ya rasa ransa yayin da wasu yan uwan juna su 3 suka jikkata da munanan raunuka biyo bayan fashewar wani abu da ake zaton bom ne a yankin Bassa dake karamar hukumar Shiroro, ta jihar Nijer, a safiyar yau alhamis.
Daily Trust, tace laarin ya faru yayin da mutanen ke kan hanya a tsakanin Bassa da Gwadara, don zuwa girbe amfanin gona.
Mazauna inda abin ya faru sunce bom din farko ya tashi tare da jikkata mutane uku masu shekaru 20, 14, da 15, lokacin da suke tafiya akan babur wanda kafar biyu daga cikin su ta cire, sannan bom na biyu ya tashi tare da kashe Dauda.
Lokacin da aka tuntubi kakakin rundunar yan sandan jihar ta Niger, SP Wasiu Abiodun, yace zai bi diddigin lamarin, sai dai kawo lokacin rubuta wannan labari bai ce komai ba.
Kawo yanzu dai babu wata kungiyar yan ta’adda data dauki alhakin kai hari.