Rundunar Civil Defence zata baza jami’ai 3,542 a lokacin kirsimeti da sabuwar shekara a jihar Kano

0
39

Rundunar tsaron al’umma ta farin kaya Civil Defence, reshen jahar Kano ta sanar da shirin tabbatar da tsaro yayin gudanar bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekarar 2025.

Mai magana da yawun rundunar SC Ibrahim Idris Abdullahi, CDPRO, ne ya sanar da hakan cikin wata sanarwa da aka aikewa jaridar Daily News 24, a yau juma’a.

Rundunar karkashin jagorancin kwamandan ta Mohammed Lawal Falala, fcna, tace zata baza jami’an ta (3,542) a guraren bautar kiristoci da suka hadar da majami’u don basu tsaron gudanar da bikin cikin kwanciyar hankali.

An tatttaro jami’an daga daukacin shiyyoyin Civil Defence, na kananun hukumomi 44 dake Kano, inda zasu yi aiki a guraren wucewar ababen hawa da cunkoso.

Civil Defence, tace duk da haka jami’an ta zasu cigaba da bayar da tsaro a gine ginen gwamnati tsawon awanni 24, a fadin Jihar Kano, da kuma jan kunnen bata gari wajen kaucewa tayar da hankalin al’umma.

Rundunar tace duk wanda aka samu da laifin karya doka ko tayar da hankalin al’umma zai fuskanci fushin hukuma.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here