Rundunar Hisbah ta jihar Kano, ta jaddada cewa har yanzu akwai dokar hana taron biki musamman tsakanin maza da mata, da zarar karfe 11 na dare tayi.
Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr. Mujahiddin Aminudden, ne ya sanar da hakan, inda yace ana yin amfani da lokutan bukukuwa wajen lalata yan mata.
Hisbah, tace wajibi ne iyaye su rika kula da yanayin yayan su mata a lokutan bukukuwa saboda akwai maza masu yin amfani da lokacin da ake shafewa a wajen taron bukukuwa zuwa tsakar dare don kai yan mata otal da yin lalata dasu.
Hisbah ta kara da cewa a wasu bukukuwan ana iya kaiwa karfe 12 zuwa 3 na dare yan mata basu koma gida ba, kuma Wannan shine babbar hanyar da ake yin lalata da mata.
Haka zalika, rundunar Hisbah, ta jihar Kano, ta ce yanzu lokacin bukukuwan kirsimeti da karshen shekara ne don haka su kula da yayan su, da kuma inda suke zuwa da wadanda suke yin ma’amala dasu.
A wani cigaban, Hisbah ta sanar da kama wani Matukin babur mai kafa uku (Adaidaita Sahu) wanda ya samu damar lalata wata yarinya tare da kaita gidajen banza ana lalata da ita.