Shugaban rukunin kamfanonin BUA Abdulsamad Isyaka Rabi’u, ya bayyana goyon bayan sa ga manufofin tattalin arzikin da shugaban Nigeria Bola Tinubu, ke aiwatarwa, yana mai cewa aiwatar da manufofin ya zama dole duk da cewa suna da tsauri.
Abdulsamad Isyaka Rabi’u, ya bayyana hakan a jiya lokacin daya ziyarci shugaban kasar a jihar Lagos.
Sai dai a yanzu ana fuskantar yanayin tsadar rayuwa da ba’a taba fuskantar irin ta ba a Nigeria sakamakon cire tallafin man fetur da karyewar darajar naira.
Cire tallafin man da Tinubu, yayi a ranar farko da karbar mulkin sa, da karya darajar naira ya ninka hauhawar farashin kayyakin masarufi zuwa kaso 34.60, a watan Nuwamba.
Duk da haka shugaban BUA, yace aiwatar da wadannan manufofi sun zama wajibi duk da kuncin da ake ciki.
BUA yace tabbas akwai zafi a wasu manufofi amma ana bukatar su a yanzu, musamman a fannin canjin kudaden ketare, da aka mayar da shi na bai daya, sai dai yace fannin masana’antu ma na dan fuskantar koma baya saboda wasu manufofin.
Yace cire hannun gwamnati a fannin canjin kudaden ketare zai janyo hankalin masu zuba hannun da inganta masana’antu.
A bangare guda Abdulsamad Isyaka Rabi’u, yace yanayin canjin kudaden ketare ya kara tashin farashin kayan masarufi da ake sarrafawa a cikin gida.