Gwamnatin Najeriya ta musanta zarge-zargen da hukumomin jamhuriyar Nijar suka yi na cewa kungiyar ta’adda ta Lakurawa tare da taimakon jami’an tsaron kasashen waje ciki har da jami’an tsaron Najeriya ne suka kai hari kan bututun mai tsakanin Nijar da Benin a ranar 13 ga watan Disamban 2024, a garin Gaya dake jihar Dosso a jamhuriyar Nijar.
Mukaddashin mai magana da yawun ma’aikatar harkokin waje ta Nigeria, Kimiebi Imomotimi Ebienfa, ne ya sanar da hakan a yau asabar.
Yace Najeriya ta jajanta wa gwamnatin Nijar kan harin da aka kai kan bututun man, amma ta sanar da cewa mahukuntan ta ba su da goyon baya ko taimakon wadanda suka kai harin.
A cewar sanarwar Gwamnatin Najeriya ta jajirce wajen yaki da ta’addanci kuma ba za ta lamunci ko tallafa wa ayyukan irin wadannan kungiyoyi ba.
Ita ma gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna matukar damuwarta da kuma bayyana cewa babu sojojin Faransa a yankin arewacin kasar da ke shirin hargitsa gwamnatin Nijar.
Inda sanarwar ta kara da cewa wadannan zarge-zarge ba su da tushe kuma ya kamata a yi watsi da su gaba daya.
Gwamnatin tarayyar tace, yana da kyau a gane cewa a ko da yaushe alakar Najeriya da Faransa tana da kyau, kuma tana mutunta juna, da rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na wasu kasashen.
Sannan Najeriya tace za ta ci gaba da lalubo hanyoyin lumana don ci gaba da kyautata dangantakarta da Jamhuriyar Nijar domin amfanin al’ummar kasashen biyu.