Wani turmutsutsun karɓar tallafin Abincin kirsimeti, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 17 a yanki Okija, dake karamar hukumar Ihiala ta jihar Anambra.
Wani dan siyasa daga jam’iyyar APGA mai suna Chief Ernest Obiejesi, ya shirya bayar da tallafin.
Makamancin hakan ya faru a Abuja, da Oyo, wanda mutane 40, suka mutu a Oyo, Abuja kuma 10, suka mutu a yau asabar.
Ana kyautata zaton cewa yunwa da ake fama da ita a Nigeria itace sanadiyyar mutuwar mutanen, saboda cikowar al’ummar dake neman taimako.