Kungiyar tarayyar Turai EU, ta sanar da tattara Euro miliyan 1, don bayar da su a matsayin tallafi ga mutanen Nigeria da suka fuskanci ambaliyar ruwan sama a shekarar 2024.
Tuni kungiyar ta sanar da ware makudan kudaden da za’a magance matsalar da ambaliyar ta haifar, da kuma yakar cutar amai da gudawa.
Zuwa yanzu tarayyar Turai ta kashe kudaden da yawan su yakai Euro miliyan 48.7, a Nigeria cikin Wannan shekara ta 2024 da ake bankawa da ita.
Yankin arewa maso yammacin Nigeria shine yafi samun tallafin saboda ta’azarar matsalolin jin kai a yankin da suka hadar da rashin abinci mai Gina jiki, da matsalolin tsaro ya haifar, sai kuma matsalar kiwon lafiya.
Cikin kokarin tallafi ga al’ummun da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a watan Oktoba, kungiyar ta EU ta bayar da Euro dubu dari biyar (€500,000) ga jihohin Kogi, Delta, da Anambra.
Ambaliyar ruwan shekarar 2024 ta shafi dubban mutane, yayin da dubban gidaje da gonaki suka sulwanta musamman a garuruwan dake kusa da kogin Neja da Benue.
An shirya cewa tallafin na EU zai taimaka wajen samar da muhalli, tsaftataccen ruwa da tsaro ga mutanen da ambaliyar ta shafa.