Hisbah ta kamo kananun mata 10 da suka kama dakuna a Otal

0
7

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta cigaba da aikin gyara al’umma karkashin atisayen ta mai suna gyara kayan ka.

A daren jiya asabar dakarun rundunar sun yi rangadi zuwa guraren lalata tarbiyyar matasa maza da mata a birnin Kano, inda aka yiwa wadanda ba’a taba kamawa ba nasiha da Kuma kamo yan mata 10, masu kunnen Kashi.

A cikin yan matan da aka samu sun kama dakuna suna yin zaman aikata badala a Otal sun hadar da yan asalin jihar Kano, da Kuma wadanda suka zo daga jihar Bauchi.

Cikin sakon muryar mataimakin kwamandan rundunar Hisbah Dr. Mujahiddin Aminudden, da aka aikowa Daily News 24, yace halayyar kananun yaran mata abin tayar da hankalin ne, musamman yanda shaye-shaye ya lalata musu rayuwa tun daga jin muryar su.

A cikin matan da aka samu akwai wadanda aka kama sau hudu, uku, biyu Kuma har yanzu basu dauki darasin dena aikata laifin ba.

Akan haka ne rundunar Hisbah ta ke kara jan hankalin al’umma su kiyaye dokokin Allah, da kaucewa fushin sa.

Guraren da Hisbah takai samame sun hadar da;

1 VAVILA PACK KOFAR RUWA
2 BAYAN DALA
3 AIRPORT ROAD
4 ASHTAN ROAD
5 AMINU KANO WAY
6 ELGANTY HOTEL PNISAU ROAD
7 BUBBLE PLUS AIRPORT ROAD
8 BAKIN ROYAL SABON GARI
9 HAUSA ROAD SABON GARI
10 FRANCER ROAD S/GARI
11 FAGGE LAYIN DANDALI
12 IBB WAY

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here